Kwastam sun kashe wani mai shigo da shinkafa ta barauniyar hanya a Katsina

Kwastam sun kashe wani mai shigo da shinkafa ta barauniyar hanya a Katsina

- Jami'an kwastam sun kashe wani mai fasa kaurin shinkafa a Katsina

- An tattaro cewa marigayin yayi yunkurin tserewa kamu ne lokacin da ya hango jami'an

- Hakan ya sanya suka bude masa wuta wanda yayi ajalinsa

Jami’an hukumar kwastam na Najeriya sn kashe wani mutumi da ake zargi da kasancewa dan fasa kaurin shinkafa jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani idanun shaida ya bayyana cewa lamarin ya afku a jiya, Lahadi, 23 ga watan Satumba a hanyar Dutsinma, kusa da kwalejin ilimi na tarayya.

Yace marigayin wanda ya tuko mota kirar J5 Peugeot, yayi kokarin tserema kamu lokacin da ya hango jami’an kwastan wadanda suka bude masa wuta.

Kwastam sun kashe wani mai shigo da shinkafa ta barauniyar hanya a Katsina
Kwastam sun kashe wani mai shigo da shinkafa ta barauniyar hanya a Katsina
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa jami’an yan sanda sun dauke gawar marigayin wanda ba’a gano ko wanene ba a lokacin wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Osun: PDP zasu kulla yarjejeniya tare da Omisore da sauran yan takarar kujeran gwamna

Kakakin yan sandan jihar, DSP Gambo Isah, yace an dauki mutumin zuwa asibiti inda anan aka tabbatar da mutuwarsa.

Yace hukumar ta fara bincike cikin lamarin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel