Daga karshe, Atiku Abubakar ya fadi ainahin abunda ke tsakanin sa da Obasanjo

Daga karshe, Atiku Abubakar ya fadi ainahin abunda ke tsakanin sa da Obasanjo

- Atiku Abubakar ya fadi ainahin abunda ke tsakanin sa da Obasanjo

- Yace shi bai da wata matsala da shi

- Ya kuma ce amma idan shi yana da matsala da shi, wannan shi ta shafa ba ni ba

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma daya daga cikin masu neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce shi bai da matsala ko wace iri da tsohon uban gidan sa, Obasanjo.

Daga karshe, Atiku Abubakar ya fadi ainahin abunda ke tsakanin sa da Obasanjo
Daga karshe, Atiku Abubakar ya fadi ainahin abunda ke tsakanin sa da Obasanjo
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Tikitin PDP: Sule Lamido ya fadi dalilin da yasa yafi Atiku cancanta

Atiku Abubakar dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da shugabannin jam'iyyar ta PDP a jihar Nasarawa a cigaba da yakeyi na yawon sada zumunta gabanin zaben fitar da gwanin da za suyi.

Legit.ng ta samu cewa da aka tambaye shi ko meye matsalar dake tsakanin sa da tsohon shugaban kasar da yayi aiki tare da shi, sai yace: "Ni dai ban da matsala da shi, amma idan shi yana da matsala da ni, wannan shi ta shafa ba ni ba."

Haka zalika kamar a dukkan jahohin da ya je, Atiku Abubakar din ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar idan har ya zama shugaban kasa.

A wani labarin kuma, Kasa da kwana daya bayan jagoran darikar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya fito da surukin sa, Abba Kabir fom din takarar Gwamnan jihar Kano a zaben 2019, ya kuma kara fito da wasu surukan nasa biyu.

Kamar dai yadda muka samu, Sanatan da yanzu haka yake neman tikitin takarar shugabancin kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar PDP ya fito ne da surukan nasa takarar kujerun majalisar tarayya a jihar ta Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel