Rashin albashi, farin jinin Adeleke da sauran dalilan da su ka sa Adeleke ya ba APC mamaki
Yanzu haka dai Hukumar zabe na kasa watau INEC ta dage zaben Gwamnan Jihar Osun bayan an gaza samun wanda ya samu cikakkiyar nasara tsakanin Jam’iyyar APC da PDP bayan an sanar da sakamakon Karamar Hukumar Osogbo.

Asali: Depositphotos
Mun kawo dalilan da su ka sa Jam’iyyar PDP ta ba jama’a mamaki a zaben:
1. Rashin albashi
Daga cikin abin da ya hana APC samun cikakken nasara akwai matsalar da Gwamnatin Aregbesola ta samu na rashin biyan Ma’aikata albashi tun tsakiyar 2015. Sai dai kwanan ne daf da zabe aka fara biyan Ma’aikata cikakken albashi a Jihar.
2. Farin jinin Adeleke
Wani abu da ya sa PDP ta samu kuri’u rututu shi ne farin jinin Marigayi Sanata Isiaka Adeleke. Ademola Adeleke ya dare kan kujerar Sanata ne bayan rasuwar ‘Dan uwan sa Marigayi Isiaka Adeleke wanda yake da farin jini matuka a Jihar.
KU KARANTA: PDP ta tserewa APC kafin a gama tattara kuri’un zaben Osun
3. Osun ta Yamma
Mutanen Yankin Osun na Yamma sun ji dadin yadda PDP ta tsaida Ademola Adeleke domin mutanen Yankin su samu Gwamna wannan karo. Wannan na cikin dalilan da su ka sa Adeleke ya samu makudan kuri’u musamman a Yankin sa.
4. Dinke barakar PDP
PDP ta samu hada-kan manyan ‘Yan siyasar da su kayi takarar fitar da gwani a zaben na Osun. Bukola Saraki ya dinke barakar da ke tsakanin Ademola Adeleke da Dr. Akin Ogunbiyi wanda hakan ya taimakawa PDP ainun.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng