Makarfi ya karyata jita-jitar cewa ya marawa wani ‘Dan takarar Gwamna baya

Makarfi ya karyata jita-jitar cewa ya marawa wani ‘Dan takarar Gwamna baya

Da alama Jam’iyyar PDP ta shiga rikici kan wanda zai kara da Gwamna Nasir El-Rufai na Jam’iyyar APC a zaben Jihar Kaduna. Fiye da ‘Yan takara 11 ne ke harin kujerar Gwamnan a PDP.

Makarfi ya karyata jita-jitar cewa ya marawa wani ‘Dan takarar Gwamna baya
Makarfi yace duk wanda ya iya allon sa ya wanke a Kaduna
Asali: Facebook

Tsohon Gwamnan Jihar Ahmad Makarfi ya karyata rade-radin da ake yi na cewa yana tare da daya daga cikin ‘Yan takaran Gwamna a karkashin PDP a Kaduna. Makarfi yace kowa Jam’iyyar PDP ta tsaida a Jihar Kaduna na shi ne.

Sanata Ahmad Muhammad Makarfi yayi wannan jawabi ne a jiya Asabar ta bakin Hadimin sa Muktar Sirajo inda ya karyata jita-jitan cewa yana marawa wani daga cikin masu kujerar Gwamna a zaben 2019 a Jam’iyyar PDP baya.

KU KARANTA: ‘Yan takara 3 da za su iya kawowa El-Rufai ciwon kai a Kaduna

Tsohon Sanatan Jihar yace abin da yake so shi ne kurum Jam’iyyar su ta PDP ta lashe zaben 2019 a kowane mataki. Tsohon Sanatan Jihar dai yace zai yi kyau ‘Yan takarar Gwamnan su hada kai domin tika APC da kasa a 2019.

Tsohon Shugaban PDP na kasa Ahmad Makarfi ya nuna cewa dole ayi adalci wajen zaben fitar da gwani inda kowane ‘Dan takara zai jarraba sa’ar sa. Babban ‘Dan siyasar yace ‘Ya ‘yan Jam’iyya ne za su tsaida ‘Dan takarar da ya dace.

Ana tunani cewa Ahmad Makarfi yana tare da Isa Ashiru Kudan wanda ya nemi Gwamna a 2015 a APC. Yanzu dai Kudan yana cikin wanda za su kara da Sanata Sulaiman Hunkuyi da irin su Sani Bello da wasu 'Yan takaran rututu a PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel