HIV/AIDS: Aisha Buhari za ta bar Najeriya zuwa Kasar Amurka

HIV/AIDS: Aisha Buhari za ta bar Najeriya zuwa Kasar Amurka

- Aisha Buhari za ta kama hanyar zuwa Kasar Amurka domin wani babban taro

- Matar Shugaban kasar za ta halaci wani taro da aka shirya kan cutar kanjamau

- Uwargidar Shugabar Kasar Nijar Malika Issoufou ma za ta kasance wajen taron

HIV/AIDS: Aisha Buhari za ta bar Najeriya zuwa Kasar Amurka
Mai dakin Shugaba Buhari za ta halarci wani taro a New York
Asali: Depositphotos

Labari ya kai gare mu cewa yau ne Hajiya Aisha Buhari za ta bar Najeriya zuwa Garin New York na kasar Amurka domin halartar wani taro da Matan Shugabannin Kasashen Afrika watau OAFLA a kan cutar nan ta Kanjamau.

Babban Darektan yada labarai na ofishin Uwargidar Shugaban kasa Buhari watau Suleiman Haruna ya bayana cewa yau Lahadi Hajiya Buhari za ta wuce Amurka domin halartar wannan taro da aka shirya a Birnin New York.

KU KARANTA: Matar Shugaban kasa ta taimakawa wasu Mata a Katsina

An shirya wannan taro ne kusan lokaci guda da zaman Majalisar Dinkin Duniya karo na 73 da za ayi. A wannan taro na UN da za ayi a cikin Birnin na New York, Shugaban Najeriya watau Muhammadu Buhari shi ma zai yi jawabi.

Matar Shugaban Nijar watau Hajiya Malika Issoufou za ta halarci wannan babban taro inda za ayi jawabai iri-iri wajen ganin an yi maganin irin cututtukan Kanjamau da kansar mama da matsalolin haihuwa na mata a kasashen Afrika.

Matar Shugaban kasa Buhari tana cikin Jakadun yaki da cutar HIV da AIDS a Duniya. Aisha Buhari za tayi jawabi a wajen taron game da yadda za a kawo karshen wannan muguwar cuta.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel