2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna

A yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa, mata daga arewa sun zaburo domin a dama da su a takarar kujeru a jihohi da jam’iyyu daban-daban.

Alamar yunkurowar matan arewa a siyasa ta fito fili ne bayan jam’iyyu sun fara sayar da fam din takarar shiga zabukan 2019. Mata sun sayi fam din takara a jam’iyyunsu, kuma mafi yawan matan na takarar kujerar majalisar wakilan tarayya ne.

A yayin da wasu daga cikin matan har yanzu ke cigaba takara, wasu daga cikinsu sun janye bayan buga hotunan tallata kansu (fosta) bisa dalilan kashin kansu.

DUBA WANNAN: 2019: Kwankwaso ya tsayar da dan takarar gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Ba bakon wani abu bane a wasu jihohin arewa ka ga mata na yin takara a wasu jihohinb arewa, musamman jihohin arewa maso gabas da arewa ta tsakiya, wannan karon an samu mata daga jihohin arewa maso yamma da ba kasafai ake ganin mata na fitowa takara ba.

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Delu James; 'Yar takarar majalisa a APC daga jihar Adamawa
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Maria A. Leonard; mai takarar majalisar dokoki a mazabar Chikun dake jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar PDP
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Hajiya Ramatu Sabo Elleman; 'yar takarar gwamna a jihar Jigawa karkashin jam'iyyar SDP
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Munira Sulaiman Tanimu 'yar takarar majalisar dokoki ta jihar Kaduna a mazabar Lere ta Gabas a jam'iyyar PDP.
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Zainab Buba Marwa 'yar takarar majalisar wakilan Najeriya a mazabar cikin birnin Abuja (AMAC) da Bwari a karkashin jam'iyyar APC
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Aisha Augie Kuta Argungu; 'yar takarar majalisar wakilai ta tarayya a jam'iyyar APC.
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Mnena Ikondo Ikpa; 'yar takarar majalissar wakilan Najeriya a mazabar Kwande da Ushongo a Benue a karkashin jam'iyyar PDP
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Gimbiya Saratu Sarki Bello; 'yar takarar majalisar dokokin jihar Niger a mazabar Paikoro a karkashin jam'iyyar APC
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Bilkisu Abubakar Siddiq; 'yar takarar majalisar dokokin jihar Adamawa a mazabar Girei a jam'iyyar APC
Asali: Depositphotos

2019: Matan arewa 10 dake takarar shugabanci da jam’iyunsu, hotuna
Aisha Ibrahim Waziri, 'Ya takarar majalisar wakilan tarayya a mazabar Jere ta jihar Borno a jam'iyyar APC.
Asali: Depositphotos

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel