Yanzu-yanzu: Jama'a sun hana jami'ar PDP wucewa sai ta cika alkawarinta na sallamarsusu

Yanzu-yanzu: Jama'a sun hana jami'ar PDP wucewa sai ta cika alkawarinta na sallamarsusu

Rikici ya barke a yanzu a Unit 2, Ward 8, Kobo a garin Osogbo, jihar Osun yayinda mutane suka tare wata jam'iar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun hana ta tafiya gida bayan kammala zabe sai ta biyasu kudi kamar yadda ta musu alkawari.

Sun bayyana cewa tayi musu alkawarin cewa za ta basu kudi muddin suka zabi jam'iyyar PDP a yau.

Game da cewar idon shaida, an rubuta sunayen mutanen ne cikin wani takarda kafin su kada kuri'arsu.

Amma bayan kamalla zabe da kirga kuri'un, an lallasa jami'yyar PDP a wajen. Kawai sai jami'in PDP ya arce kawai. Da jama'an suka ga abokiyar aikinsa, sai suka tirke ta.

Yanzu-yanzu: Jama'a sun hana jami'ar PDP wucewa sai ta cika alkawarinta na sallamarsusu
Yanzu-yanzu: Jama'a sun hana jami'ar PDP wucewa sai ta cika alkawarinta na sallamarsusu
Asali: Facebook

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa rundunar yan sanda sun samu nasarar cafke wasu jami'an jam'iyyar PDP guda biyu a kokarin da suke yi na sayen kuri'u a zaben gwamnan jihar Osun da ake kan gudanarwa yanzu.

Wannan na daga cikin yunkurin da hukumar INEC ta ke yi na gudanar da sahihin zabe. Bisa wannan rahoto da rundunar ta samu, kodinetan tsaro a zaben, Joshak Habila, wanda shine mataimakin Sifeta Janar na rundunar yan sanda DIG, ya bayar da umurnin cafke su da zaran an gansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel