Gabanin zabe, gwamna Elrufai zai biya malaman Kaduna kudaden da suke bin gwamnati
- Gwamnatin jihar Kaduna zata biya sababbin malamai kudaden su
- An tabbatar da karatun yara mata kyauta a jihar
- An maida biyan albashin malamai SUBEB, maimakon karamar hukuma

Asali: Twitter
Gwamnatin jihar Kaduna tayi alkawarin biyan sababbin malamai duk kudin da suke bi nan da karshen watan satumba.
Kwamishinan ilimi na jihar, Ja'afaru Sani, ya fadi hakan a gurin horar da malaman firamare da akewa malaman akan Jolly Phonics teaching methodology wanda Universal Learning Solutions da hadin guiwar SUBEB reshen jihar Kaduna suka hada a ranar juma'a.
Yace an yanke shawarar biyan malaman kudin da suke bi ne bayan taron da sukayi da Gwamna Nasir Elrufai akan maganar a ranar litinin.
Gwamnan ya maida biyan albashin malamai SUBEB daga kananan hukumomin su.
Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnan ya tabbatar da ilimin yara matan sakandaren jihar kyauta.
DUBA WANNAN: An biya 'yan NEPA kudadensu na bashi daga Tarayya
Yayi bayanin cewa gwamnatin jihar ta yanke shawarar cire duk wani abu da zai zama kalubale ga karatun mata a matsayin su na ginshikin al'umma.
Yace ma'aikatar su ta aikawa da ofisoshin yankunan jihar da makarantun sakandare umarnin tabbatar da ilimin kyauta
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng