An cafke wasu masu yiwa shugaban 'yan sanda kazafi
Hukumar 'yan sanda ta damke wasu mutane uku da su suka rika bin gidaje da filaye suna saka alamar cewa gidajen mallakar Sufetan 'yan sanda, Ibrahim Idris ne a wasu unguwanni da ke jihar Legas.
Mutanen sune Williams Iyeke, Julius Babasola da Olufemi Ogundare. Ana kuma neman wani Soji Adeniyi wanda shine ya samar musu da takardun masu dauke da tambarin hukumar 'yan sanda da sunan Sufeta, Ibarhim Idris.
An kama Williams Iyeke da Julius Babasola suna mana takardan bogi mai dauke da tambarin 'yan sanda mai dauke da rubutu cewa "wannan filin mallakar sufeta janar na 'yan sanda, IGP Idris Abubakar ne" wasu filaye da ke Adewale Kuku Street, Ademfemi Cresecent Street, Akande Street, Owolabi Salisu Crescent da ke Millenium Estate Oke Alo, Gbagada a jihar Legas.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda na kasa, Moshood Jimoh ya ce sunan Sufetan 'yan sanda IGP Ibrahim K. Idris ba IGP Idris Abubakar kamar yadda 'yan damfarar suka rubuta ba kuma ya ce IG ba shi da wata fili ko gida a Millenium Estate, Gbagada a Legas.

Asali: Facebook
Hukumar 'yan sandan ta bukaci Soji Adeniyi ya kai kansa ofishin hukumar da ke Abuja a ranar 25 ga watan Satumban 2018 indan kuma ba haka ba za'a bayar da umurnin 'yan sanda su bazama nemansa ruwa a jallo.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Za'a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng