Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa

Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa

Sabon rikici ya balle a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Zamfara, hakan yayi sanadiyar samun rabuwar kai tsakanin gwamnan jihar, Abdulaziz Yari da mataimakinsa, Ibrahim Wakkala.

Hakan na zuwa ne bayan da wasu daga cikin masu son jam'iyyar ta tsayar da su takara suka yi zargin cewa gwamnan ya dade da zabar wanda yake so ya gaje shi, kuma yake kokarin turasasa shi a kan al'umma, hakan ya sa mataimakin gwamnan tare da wasu 'yan takarar guda bakwai suka nuna turjiya akan wannan yunkuri nasa.

Mataimakin gwamnan, ya shaida wa manema labarai cewa idan har gwamna Yari ya zabi wanda zai gaje shi, ba zai hana wasu 'yan takara su tsaya ba.

Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa
Sabani ya shiga tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa
Asali: Depositphotos

Ya kuma yi zargin ba za a yi adalci kan salon zaben wakilai da ake son gudanarwa a zaben da ke tafe ba.

Hakazalika ya bukaci a gudanar da zabe na kato bayan kato idan har ana son yin adalci.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai: An tashi baram-baram a wani zaman sulhu tsakanin 'yan takarar shugaban kasa a PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, tunanin wanda zai zamo gwamnan jihar Legas na gaba zai iya kawo rabuwar kawuna tsakanin shugabancin kasa, gwamnonin APC da kuma shugaban jam'iyyar APC ta kasa Bola Ahmed Tinubu da magoya bayan shi.

Tinubu ya janye goyon bayan Ambode domin sake darewa kujerar shugabancin jihar Legas sabo wani tsohon kwamishinan kasuwanci da masana'antu, Mista Babajide Sanwo-Olu.

An matsawa shugaban jam'iyyar da ya canza ra'ayi. Gwamnonin sun shawarci shugaban kasa da kada ya bar Tinubu ya guji Ambode wanda suke kira da 'Gwamnan Gwamnoni'.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel