Yanzu-Yanzu: Motar 'yan agaji daga Jos zuwa Kaduna ta samu mummunan hatsari

Yanzu-Yanzu: Motar 'yan agaji daga Jos zuwa Kaduna ta samu mummunan hatsari

- Motar 'yan agaji daga Jos zuwa Kaduna ta samu mummunan hatsari

- Hatsarin ya zo da sauki, ba samu rasuwa ba

- Daya daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su ne ya sanar da hakan

Labarin da muke samu yanzu da dumin sa na nuni ne da cewa wata mota dauke da 'yan agajin kungiyar Izala mai hedikwatar ta a garin Jos sun samu mummunan hatsari akan hanyar su ta zuwa garin Kaduna domin taimakawa mahajjatan da ke dawowa daga kasa mai tsarki.

Yanzu-Yanzu: Motar 'yan agaji daga Jos zuwa Kaduna ta samu mummunan hatsari
Yanzu-Yanzu: Motar 'yan agaji daga Jos zuwa Kaduna ta samu mummunan hatsari
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wani Lauya ya maka Buhari da Buratai kotu

Wannan dai na kunshe ne a cikin wani rubutu da daya daga cikin 'yan agajin ya rutsa da shi mai suna Muhammad Kabir Adamu ya wallafa a kan shafin sa na dandalin sadarwar zamani na Facebook jim kadan bayan aukuwar lamarin.

Legit.ng ta samu cewa hakazalika rubutun na Muhammad Kabir Adamu ya bayyana cewa aka=wai mataimakin Daraktan kungiyar a cikin wadanda hatsarin ya rutsa da su amma kuma ba'a samu rashin rai ko daya ba.

Yan agajin dai da hatsarin ya rutsa da su sun fito ne daga kananan hukumomin Kanam da kuma Jos ta Arewa kamar dai yadda muka samu.

Muna yi musu addu'ar Allah ya basu lafiya ya kuma cigaba da tsare mu baki daya. amin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel