Dalilin da ya sa na ke binciken Sanata Adamu - Gwamna Al-Makura

Dalilin da ya sa na ke binciken Sanata Adamu - Gwamna Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya bayyana cewa ya na binciken Sanata Abdullahi Adamu ne, saboda sai yanzu ake ta gano wadansu harkalla da asarkalar kudade da ya yi a lokacin da ya ke a matsayin gwamnan jihar.

Adamu mai wakiltan yankin Nasarawa ta yamma a majalisar dattawar kasar ya na daya daga cikin Sanatoci ‘yan-gani-kashe-nin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Kuma shi ne ma gagarabadau din Sanatocin da ke adawa da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, masu son ya sauka ko su tsige shi da karfin tuwo.

Dalilin da ya sa na ke binciken Sanata Adamu - Gwamna Al-Makura
Dalilin da ya sa na ke binciken Sanata Adamu - Gwamna Al-Makura
Asali: Depositphotos

Daya ke magana da manema labarai a Abuja, bayan tantance shi a matsayin dan takarar sanata, Al-Makura ya ce ita gwamnati mulki ne da ake yi a sarari, ba a boye ba, don haka wata fatarar ita ke tayar da tsohon bashi.

A cewar shi wannan dalili ne ya sa ake binciken Adamu, wanda a yau shekaru 11 kenan rabon sa da mulki.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa, a daren ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba an ambaci sunan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, a matsayin shugaban kwamitin mutane 10 da zasu tantance yan takarar kujeran shugaban kasa 13 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

KU KARANTA KUMA: Zaben Osun: INEC ta rarraba kayayyakin zabe yayinda aka tsaurara matakan tsaro

Sauran mambobin kwamitin sun hada da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar dattawa, Iyorchy Ayu, da Cif Tom Ikimi.

Haka zalika akwai Cif Okwesikizie Nwodo, Hajia Ina Ciroma, Misis Kema Chikwe, Dr Haliru Bello, Cif Ebenezer Babatope da kuma Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel cikin kwamitin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel