2019: Sambo zai tantance Saraki, Atiku, Tambuwal da sauransu

2019: Sambo zai tantance Saraki, Atiku, Tambuwal da sauransu

A daren ranar Alhamis, 20 ga watan Satumba an ambaci sunan tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, a matsayin shugaban kwamitin mutane 10 da zasu tantance yan takarar kujeran shugaban kasa 13 na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Sauran mambobin kwamitin sun hada da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar dattawa, Iyorchy Ayu, da Cif Tom Ikimi.

Haka zalika akwai Cif Okwesikizie Nwodo, Hajia Ina Ciroma, Misis Kema Chikwe, Dr Haliru Bello, Cif Ebenezer Babatope da kuma Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel cikin kwamitin.

2019: Sambo zai tantance Saraki, Atiku, Tambuwal da sauransu
2019: Sambo zai tantance Saraki, Atiku, Tambuwal da sauransu
Asali: Depositphotos

Yan takaran da za’a tantance sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa.

Sauran sun hada da Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark; a tsohon ministan ayyuka na mussaman, Alhaji Tanimu Turaki (SAN); tsohon gwamnan jihar Plateau, Sanata Jona Jang; da kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi.

KU KARANTA KUMA: Zaben Osun: INEC ta rarraba kayayyakin zabe yayinda aka tsaurara matakan tsaro

Sauran mutanen da ake sanya ran gani a taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido; Dr Datti Baba-Ahmed da Usifo Stanley.

Za’a gudanar da tantancewar a hedkwatar jam’iyyar a ranar Litinin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng