Ambode da wasu a Gwamnatin Legas na kokarin karbe APC daga hannun Tinubu

Ambode da wasu a Gwamnatin Legas na kokarin karbe APC daga hannun Tinubu

- Wasu kusoshi a Gwamnatin Ambode na kokarin kawo karshen Tinubu a Legas

- Wannan ne sanadiyyar rigimar Gwamnan Jihar da kuma tsohon Mai gidan na sa

- Yanzu haka dai ana kishin-kishin din cewa Tinubu ya juyawa Ambode baya a 2019

Ambode da wasu a Gwamnatin Legas na kokarin karbe APC daga hannun Tinubu
Akwai masu neman bizne siyasar Tinubu a Gwamnatin Ambode
Asali: Twitter

Mun samu labari cewa Gwamna Akinwumi Ambode yana kokarin batar da Asiwaju Ahmed Tinubu daga siyasa a 2019 da zarar ya zarce kan kujerar Gwamnan Jihar Legas. Wannan ne dai ya jawo rigima tsakanin ‘Yan siyasar.

Wasu Majiyoyi masu karfi sun nuna cewa Ambode ya shirya yadda zai bizne Tinubu da zarar ya zarce kan kujerar Gwamna ne a 2019. Ambode ya shirya wannan aiki ne da wani babban Hadimin sa Bunmi Ariyo da kuma wasu na kusa da shi.

Daga cikin wadanda ke neman kawo karshen siyasar tsohon Gwamnan na Legas akwai Kwamishinan shari’a na Jihar a yanzu Niji Kazeem wanda yake kokarin karbe APC a Legas daga hannun Tinubu wanda da ita ‘Dan siyasar ya dogara.

KU KARANTA: Tinubu na kokarin tursasa Ambode janyewa daga takara

Niji Kazeem ya shirya yadda zai karbi mulki daga hannun Ambode da zarar ya kammala wa’adin sa a 2023. Tinubu dai su ne manyan APC tun bayan da aka kafa ta. Yanzu dai ta kai Gwamna Ambode bai iya komai sai da bakin Kazeem da Ariyo.

Wani na-kusa da tsohon Gwamnan na Legas ya bayyanawa The Guild cewa wannan yunkuri na jawo Kwamishin shari’an ne ya kawowa Ambode matsala da Tinubu. Kazeem ne dai ya jawo yadda aka fara ware yaran Tinubu a Gwamnatin Legas.

Majiyar ta kuma bayyana cewa Niji Kazeem yayi kutun-kutun ne aka nada sa kan wannan kujerar duk da akwai wanda su ka fi sa kwarewa domin ya yaki Tinubu zuwa 2023. Kazeem yana kurin cewa zai takawa Tinubu burki a Legas bayan 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel