Jam’iyyar PDP ta tantace masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019

Jam’iyyar PDP ta tantace masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019

Mun samu labari cewa babbar Jam’iyyar adawar Najeriya PDP ta tantace da-dama daga cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019 inda ‘Yan takara sama da 10 su ka fito ake kuma neman tsaida mutum guda rak.

Jam’iyyar PDP ta tantace masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019
PDP za ta tantance Sule Lamido da Kwankwaso
Asali: Depositphotos

A jiya Jam’iyyar PDP ta tantance ‘Yan takarar ta da ke neman bugawa da Shugaban kasa Buhari a zaben Shugaban kasa. Wadanda aka tantance sun hada da Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal, da kuma Sanata Jonah Jang.

Sauran wadanda Jam’iyyar ta tantance a Maitama da ke Babban Birnin Tarayya kamar yadda mu ka samu labari daga manema labarai, sun hada da Ahmed Muhammad Makarfi, Sanata Datti Baba-Ahmed da kuma Attahiru Bafarawa.

Shugaban Majalisa Bukola Saraki ne aka fara tantancewa a jiya, bayan ya fito ya nuna cewa Jam’iyyar ta PDP ta shiryawa 2019 kuma ta kama hanyar gudanar da zaben kwarai domin fitar da ‘Dan takarar ta na Shugaban kasa a zaben na gaba.

KU KARANTA: PDP tayi wani zaben somin-tabi domin shiryawa 2019 a Katsina

Kwamitin da ke wannan aiki yana karkashin jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo ne. Shi ma wani tsohon Mataimakin Shugaban kasar Atiku Abubakar ya nuna gamsuwar kwarai da tantancen sa da aka yi jiya.

A jiya ne dai tsohon Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso wanda yana cikin ‘Yan takarar ya shiga Jihar Kano a gurguje domin ya gana da manyan PDP na Jihar. Watakila hakan ya sa ba a tantance Kwankwaso ba a dalilin makara da yayi.

Ana sa rai yau PDP ne za ta tantance tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido da Sanatan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da kuma irin su Kabiru Tanimu Turaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel