Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna

Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna

- Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar gano wasu makudan kudade da suka kai dala milyan 470.5m, mallakin kamfanin NNPC Brass LNG

- Rundunar ta sake lissafa wasu nasarori da ta samu, na gano N114,290,000, daga wajen wasu jami'an hukumar INEC guda 23

- Rundunar ta bayyana himmatuwarta na yaki da masu durkusar da tattalin arzikin kasar, musamman ma barayin man fetur

Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar gano wasu makudan kudade da suka kai dala milyan 470.5, mallakin kamfanin NNPC Brass LNG da aka boye su a wasu bankuwan kasuwa daban daban a Nigeria.

Babban abun daure kan shine, rundunar yan sandan ta ce ta sake gano wasu makudan kudaden da suka kai N8,807,264,834.96, mallakin NNPC Brass LNG a wasu bankunan daban.

A cewar rundunar yan sandan, an samu nasarar gano kudaden ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin mayar da duk kudaden gwamnati a cikin asusu daya TSA.

KARANTA WANNAN: Sabuwar badakala: PDP ta ce an karkatar da kudin jirgin Nigeria Air don yakin zaben Buhari a 2019

Rundunar wacce ta jinjinawa sashe na musamman wanda Sife Janar ya samar don kula da muhimman ayyuka da suka shafi ta'addanci, sata ta yanar gizo ko aikata laifuka a yanar gizo, ba ta bayyana lokacin da ta gano wadannan kudade ba.

Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna
Rundunar yan sanda ta gano $470.5m mallakin NNPC Brass LNG da aka boye a bankuna
Asali: Facebook

Sai dai rundunar ta sake lissafa wasu nasarori da ta samu, na gano N114,290,000, daga wajen wasu jami'an hukumar INEC guda 23 a ranar 10 ga watan Disamba, 2016, a lokacin da ake tsaka da sake gudanar da zaben jihar Rivers.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, Jimoh Mashood, inda rundunar ta bayyana himmatuwarta na tona asirin mutanen da ke durkusar da tattalin arzikin kasar, musamman ma barayin man fetur.

Rundunar ta ce a kokarin ta na yaki da masu gurguntar da tattalin arziki da kuma masu lalata bututun mai da ma satar man, rundunar ta kwato kananan jiragen ruwa masu gudu, motar katako guda 83, motocin alfarma da suka hada da Jeep guda 25, bas bas guda 36, kekuna guda 29, da kuma mashinan hako mai guda 38.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel