An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9

An kama sojojin da suka kashe yar shekara 9

Rundunar 'yan sanda sun sanar da cewan an damke wasu sojoji hudu a Somaliya bayan da aka harbe wata 'yar shekara tara a babban birnin kasar Mogadishu.

Kungiyar kare hakkin dan adam Amnesty International ta ce Deqa Dahir ta mutu, kuma wata yarinyar ta ji rauni lokacin da harsasai suka bula motar makarantar da ke dauke da su a cunkoson ababen hawa.

Kungiyar ta kara da cewa sojojin sun bude wuta ne a yunkurinsu na samarwa motarsu hanya.

Shugaban Somaliya ya gana da iyalan marigayiyar, a yayin da jama'a ke nuna fushinsu kan harbin da aka yi.

An binne yarinyar a ranar Alhamis, kwana biyu bayan da aka kashe ta.

KU KARANTAN KUMA: Mutum 10 sun mutu sadda fada ya kaure a wajen taron jiga-jigan jam'iyyar APC

Yarinyar dai tana shekararta ta farko ne a makaranta, kuma tana kan hanyarta ta komawa gida ne cike da farin ciki, tana shan ayis kirim, a lokacin da aka harbe ta.

Harsashin ya same ta a kai ne inda ta mutu nan take.

Mahaifinta ya nemi gwamnatin Mohamed Abdullahi Mohamed ta bi masa hakkinsa.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sanda ta bayyana cewa ta samu nasarar gano wasu makudan kudade da suka kai dala milyan 470.5, mallakin kamfanin NNPC Brass LNG da aka boye su a wasu bankuwan kasuwa daban daban a Najeriya.

Babban abun daure kan shine, rundunar yan sandan ta ce ta sake gano wasu makudan kudaden da suka kai N8,807,264,834.96, mallakin NNPC Brass LNG a wasu bankunan daban.

A cewar rundunar yan sandan, an samu nasarar gano kudaden ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin mayar da duk kudaden gwamnati a cikin asusu daya TSA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng