Yan bindiga sun yi garkuwa da karamin yaron shugaban jam’iyyar APC daga makaranta

Yan bindiga sun yi garkuwa da karamin yaron shugaban jam’iyyar APC daga makaranta

Rundunar yansandan jahar Borno ta sanar da sace yaron shugaban jam’iyyar APC na jahar Borno Ali Bukar Dalori mai shekaru hudu a rayuwa a ranar Laraba 19 ga watan Satumba, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Damian Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, inda yace masu garkuwan sun sace yaron ne daga makarantar Maiduguri Capital School, dake garin Maiduguri.

KU KARANTA: Zaben shugaban hukumar kwallon kafa: Yadda Amaju ya sake zarcewa a Katsina

Kwamishinan ya kara da cewa har yanzu babu wanda ya san inda aka tafi da yaron, amma yace rundunar yansandan jahar ta kaddamar da cikakken bincike akan lamarin don ganin ta tseratar da yaron daga hannun masu garkuwan.

Kwamishina ya cigaba da jan kunnen yan siyasa daga daukan duk wani mummunan mataki akan abokan hamayyarsu a siyasance don wai su cimma wata manufarsu. “Wannan kira ne ga yan siyasa dasu bude idanunsu.

“Ya zama wajibi yan siyasa su shiga taitayinsu tare da kulawa sosai kuma su sanya idanu akan yayansu a kowanne lokaci, sa’annan su kai karar duk wani wanda suke zargi ga jami’an hukumomin tsaro.” Inji shi.

Zuwa yanzu dai iyayen wannan yaro na cikin bakin ciki, yayin da yan uwa da abokan arziki ke cigaba da kwarara gidan suna tayasu alhinin wannan lamari, tare da fatan Allah ya bayyana shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel