Gwamnatin Tarayya ta dawo da wanda aka kora daga aiki a 2013

Gwamnatin Tarayya ta dawo da wanda aka kora daga aiki a 2013

Gwamnatin Tarayya ta nemi a dawo da wani Jami’in Gwamnati mai suna Yushau Shuaib daga aiki bayan an kore sa ba bisa hakki ba inda aka yi masa ritaya da karfi da yaji a shekarar 2013.

Gwamnatin Tarayya ta dawo da wanda aka kora daga aiki a 2013
A 2013 aka kori Yushau Shuaib bayan ya soki Okonjo-Iweala
Asali: Depositphotos

A 2013 ne Gwamnatin Tarayya tayi wa Yushau Shuaib ritaya bayan ya kai mataki na 14 a Gwamnati. Tun a lokacin ne Ma’aikacin ya shiga Kotu inda ya rika shari’a da Gwamnati. Yanzu dai an nemi a dawo da Ma’aikacin bakin aiki.

Yanzu dai wata wasika mai lamba FMIC/LEG/307/VOL.1/122 ta fito daga Ma’aikatar yada labarai wanda Darektan Ma’aikatar S.U. Ewa ya sa hannu. An nemi a maida Shuaibu bakin aikin sa a yanzu cikin gaggawa ba tare da bata lokaci ba.

KU KARANTA: 2019: Matasa na ke wakilta a Najeriya – Jerry Gana

Takardar ta nemi a dawo da Yushau Shuaibu ofis ne a dalilin hukuncin da Kotu tayi a karshen 2017 inda ta bayyana cewa an kore sa ne ba bisa hakki ba. Shekaru kusan 4 kenan babban Ma’aikacin yayi yana fafatawa a gaban shari’a.

An kori Mista Shuaibu ne a dalilin wani rubutu da yayi wanda ya taba Ministar kudi ta lokacin Ngozi Okonjo-Iweala. Shuaibu yana ikirarin cewa dokar aikin kasa ta ba shi damar yayi rubutu ya wallafa a Jarida ko da ya taba Jami’an Gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel