APC ta canza ranakun da za a gudanar da zaben fitar da gwani
Labari ya kai gare mu cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole da Majalisar sa watau NWC ya gana da Sanatocin APC domin sake yi wa jadawalin zaben 2019 kallon karshe.

Asali: Twitter
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa ya zauna da ‘Yan Majalisan APC ne domin canza ranar da za a gudanar da zaben fitar da gwani na Jam’iyya. Yanzu dai APC za ta yi zaben tsaida ‘Yan takara ne a karshen wannan Watan na Satumba.
Sakataren tsare-tsare na Jam’iyyar APC na kasa baki-daya watau Emma Ibediro ya sanar da cewa an sake ranakun da za ayi zaben fitar-da-gwani. Yanzu dai an maida zaben Gwamnonin Jihohi zuwa Ranar 2 ga Watan gobe na Okotoba.
KU KARANTA: Yakubu Dogara ya isa Hedikwatar Jam'iyyar PDP
Emma Ibediro ya kuma bayyana cewa za a tsaida ‘Dan takarar Shugaban kasa ne a Ranar 25 ga Watan Satumba. Za kuma ayi zaben Gwamnoni ne yanzu a Ranar 29 ga Watan Satumba kamar yadda Uwar Jam’iyya ta sanar a makon nan.
Har wa yau za a tsaida ‘Yan takarar Majalisar Wakilai ne a Ranar 3 ga Watan Oktoba a maimakon karshen Satumba da aka shirya. APC za ta fitar da wadanda za ta ba tutan Majalisar dokoki na Jihohi ne a Ranar 4 ga Watan Okotoban.
Yayin da ake shirin zaben sabon Gwamna a Jihar Osun, mun samu labari cewa Shugaban Jam’iyar APC mai mulki na kasa baki daya watau Adams Oshiomhole ya caccaki ‘Dan takarar PDP wanda yace bai san komai ba sai tika rawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng