Zainab Ahmed ministar kudi ce – Fadar shugaban kasa

Zainab Ahmed ministar kudi ce – Fadar shugaban kasa

- Fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Zainab Ahmed zata yi aiki a matsayin ministar kudi ne kawai

- Kakakin shugaba Buhari, Femi ya bayyana cewa zata ajiye tsohuwar matsayinta na karamar ministar kasafi da tsare-tsaren kasa

- Zainab dai maye gurbin Kemi Adeosun ne bayan tayi murabus

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Zainab Ahmed wacce aka dauko daga ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare kasa zuwa ma’aikatar kudi bayan murabus din Misis Kemi Adeosun, zata bar matsayinta na baya.

Adeosun ta yi murabus a makon da ya gabata biyo bayan rade-radi cewa ta mallaki takardan NYSC dinta ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya mayar da Zainab Ahmed ma’aikatar kudi daga na kasafin kudi da tsare-tsare, inda zata yi jagoranci a matsayin ministar kudi.

Zainab Ahmed ministar kudi ce – Fadar shugaban kasa
Zainab Ahmed ministar kudi ce – Fadar shugaban kasa
Asali: Depositphotos

An samu sabanin ra’ayi kan ko zata hada matsayin biyu na ma’aikatar kasafin kudi da sabon matsayinta.

A wajen taron zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a jiya, Laraba, 18 ga watan Satumba, Zainab ta zauna ne akan kujerar Adeosun a zangon majalisar.

KU KARANTA KUMA: Za a hukunta masu yi wa mata saki uku a lokaci guda a kasar Indiya

Da yake kwance kullin bayan taron FEC, kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa Zainab zata ajiye tsohuwar mukaminta a matsayin karamar ministar kasafi, sannan zata zama shugabar ma’aikatar kudi, don haka matsayinta na yanzu shine ministar kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel