Da biyu: Gwamnan APC ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna da ya bar mulki tun 2003

Da biyu: Gwamnan APC ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna da ya bar mulki tun 2003

Rikicin da ke tsakanin gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura, da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Adamu, ta dauki sabon salo bayan gwamna mai ci ya kafa kwamitin binciken yadda tsohon gwamnan ya gudanar da wasu aiyuka lokacin yana mulki.

Gwamna Al-Makura ne ya bayyana hakan yau, Laraba, fadar gwamnatin jihar Nasarawa dake Lafiya yayin rantsar da wasu sabbin manyan sakatarorin gwamnati uku da masu bashi shawara uku. Gwamnan ya ce da zai rantsar kwanan nan zai binciki aiyukan gwamnatin baya daga shekarar 1999 zuwa 2011.

Da biyu: Gwamnan APC ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna da ya bar mulki tun 2003
Da biyu: Gwamnan APC ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamna da ya bar mulki tun 2003
Asali: Twitter

Jaridar Daily trust ta rawaito cewar kwamitin zai binciki yadda gwamnatin tsohon gwamna Abdullahi Adamu tayi gwanjon wasu kadarorin gwamnati da suka hada da Sabon Otal din garin Keffi , Otal din Conference, da Kulob din Lafia da Keffi.

DUBA WANNAN: Gwamnati ta rufe gonar Obasanjo

Kwamitin zai binciki yadda gwamnatin tsohon gwamnan ta gaza kamala wasu aiyuka da suka hada da cibiyar samar da wuta daga ruwa da kuma batun bayar da filayen noma ga ‘yan kasar Zimbabwe. Kwamitin zai bawa gwamnati shawara tare da adadin kudin da aikin zai ci kafin ya kammalu.

A cewar Almakura, Nasarawa mallakar mutanen jihar ne a saboda haka ba zai barta hannun wasu tsirarun mutane da sai yadda suke so za ai ba.

Al-Makura ya nuna fushinsa bisa yadda wasu ‘yan siyasa a jihar suka ci kare su babu babbaka a baya kuma yanzu suka zake a jam’iyyar APC wajen nuna su nagari ne ba.

Kokarin jaridar Daily Trust na jin ta bakin tsohon gwamna Adamu, a kan kwamitin da gwamna Al-Makura ya kafa domin bincikensa, bai yiwu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel