Dukan mahaifi: Kotu ta aike da wani dan asara zuwa gidan yari

Dukan mahaifi: Kotu ta aike da wani dan asara zuwa gidan yari

Wata kotu da ke zamanta a Karmo Grade 1 Abuja ta bayar da bawa wani Joseph Omonigho matsuguni a gidan yari saboda ana zarginsa da dukkan mahaifinsa.

Alkalin kotun, Inuwa Maiwada ne ya bayar da umurnin a ranar Laraba, inda ya ce a cigaba da tsare Omonigho har zuwa ranar 3 ga watan Octoba da za'a saurari shari'ar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa ana tuhumar Omonigho da ke zaune a Kado, Abuja da aikata laifuka guda hudu wanda suka hada yiwa mutum rauni, duka da cigaba da tayar da fitina.

Dukan mahaifi: Kotu ta aike da wani dan asara zuwa gidan yari
Dukan mahaifi: Kotu ta aike da wani dan asara zuwa gidan yari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe wani hadimin gwamnan Najeriya

Sai dai wanda akayi kararsa ya ce bai aikata laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

A baya, mai shigar da kara a kotu, Ijeoma Ukagha ya shaidawa kotu cewa wani David Omonigho da ke zaune a Kado Abuja ya shigar da karar kan Joseph a caji ofis na Life Camp da ke Abuja a ranar 5 ga watan Satumba.

Mai shigar da karar ya ce wanda ya yi karar ya yi ikirarin cewa dan sa yana dukansa har ya y masa rauni a fuska.

Ukagha ya ce mahaifin yaron ya ce wannan ba shine karo na farko da dansa ke dukkansa da sauran mutanen gidan ba duk da irin gargadin da akayi masa.

Mai shigar da karar ya ce laifin ya sabawa sashi na 263, 265, 244 da 199 na Penal Code.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel