Arewa: Masana sun kadu bayan da aka kula ashe yara har sun fara kwaikwayar yakin 'Soja da Boko Haram'

Arewa: Masana sun kadu bayan da aka kula ashe yara har sun fara kwaikwayar yakin 'Soja da Boko Haram'

- Yara da yawa sun zama marayu saboda yakin

- Akwai damuwa da ake kira PTSD wadda kan taba kwakwalwarsu

- Yakin ya kai shekaru kusan 10 ana yi

Arewa: Masana sun kadu bayan da aka kula ashe yara har sun fara kwaikwayar yakin 'Soja da Boko Haram'
Arewa: Masana sun kadu bayan da aka kula ashe yara har sun fara kwaikwayar yakin 'Soja da Boko Haram'
Asali: Depositphotos

Bayan da masana suka gano cewa akwai cutar kwakwalwa dake iya damun yara wadanda yaki ya shafa, a yanzu an gano akwai irin wannan matsalar a sansanonin 'yan gudun hijira, inda yara kan bada labarin an yanka iyayensu a gabansu.

Matsalar, na iya haiar musu da damuwa, zafin rai ko kuma rashin iya nutsuwa a lokutan karatu a makaranta.

Cutar PTSD, watau Post Traumatic Stress Disorder, kan shafi tsofin soji da sauran jama'a wadanda suka kadu da bala'in yaqi ko bala'i.

DUBA WANNAN: Ibrahim Mantu zai sulhunta 'yan PDP a Plateau

An kula yara da yawa a sansanonin 'yan gudun hijira sun farfado daga watandar da yan Boko Haram suka yi a yankin.

An kuma kula wai har yaran kanyi wasan yaki, inda sukan nuna wani da hannu kamar bindiga su yi harbi, wannan yace shi soja ne, wannan yace shi dan Boko Haram ne, a sansanin na Yola.

Da aka tambayi wani daga cikin yaran cewa ma yayi shii yana so ya zama soja don ya kama Boko Haram ya kashe, shekararsa 13. Yace a gabansa suka yanka kakansa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel