An baiwa Ibrahim Mantu wuqa da nama ya zabo dan takarar sulhu a PDP
- Rashin hadin kai ya ja mana rasa kujerar gwamna a jihar
- Dole ne mu fitar da wanda zai yiwa Dalong warwas
- Yiwa APC kaye shine burin mu

Asali: UGC
Reshen jam'iyyar PDP ta jihar Filato ta kafa kwamitin mutum biyar don tataunawa da 'yan takara 10 masu neman kujerar gwamnan jihar karkashin inuwar jam'iyyar don tsaida mutum daya ko rage masu neman.
Jam'iyyar ta ware kujerar don yankin kudancin jihar domin kada Simon Lalong na jam'iyyar APC, wanda shima daga yankin yake kuma Dan takarar kujerar a APC.
Duk da haka, mutanen da ke neman kujerar 8 ne daga yankin. Sun hada da: Samuel Abashe, Samuel Jatau, Jeremiah Useni, George Shitgurum, Kemi Nshe, Ibrahim Ponyah, Vitalis Maimako da Musa Gambo.
DUBA WANNAN: An sake kai hari a Kaduna
Domin gujewa kuskuren da jam'iyyar tayi a 2015, wanda ya ja rasa kujerar shugabancin jihar, jam'iyyar ta nada kwamitin da tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata, Ibrahim Mantu, cikin tataunawar kwanaki biyar da maneman kujerar, tare da samun tabbacin zasu goyi bayan duk wanda jam'iyyar ta tsayar.
Shugaban jam'iyyar a jihar, Mista Damishi Sango, yayin rantsar da kwamitin, ya horey su da adalci aikin da zasuyi domin shirin ture Gwamnatin APC.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng