Zan yi amanna da duk abin da ya faru a zaben fitar da gwani- Tambuwal
‘Daya daga cikin ‘Yan takaran 2019 watau Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana abin da zai yi idan ya fadi zaben fitar da gwani na takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP.

Asali: Depositphotos
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a wajen wani taro ya tabbatar da cewa babu abin da zai hana sa amincewa da matakin da Jam’iyyar su ta PDP ta dauka wajen bada tikitin ‘Dan takarar Shugaban kasa na zabe mai zuwa a 2019.
Rt. Hon. Waziri Tambuwal ya dai nuna cewa idan har ya samu mulkin kasar nan, zai maida hankali wjen gyara harkar tsaro musamman a Arewacin kasar nan. PDP za ta yi zaben fitar da ‘Dan takarar ta na 2019 ne a farkon wata mai zuwa.
KU KARANTA: Uzor Kalu ya nemi IBB ya marawa Buhari baya a 2019
Tsohon Shugaban Majalisar Wakilan Kasar ya fadi hakan ne a lokacin da ya gana da manyan PDP a Jihar Kebbi. A nan ne dai Tambuwal ya bayyana dalilin sa na tserewa daga Jam’iyyar APC ya koma PDP inda yace Jam’iyyar tayi kasa a gwiwa.
Gwamnan ya sha alwashin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Zamfara, Benuwai, Taraba, da irin su Birnin Gwari idan har aka zabe a a matsayin Shugaban kasa a badi. Manyan PDP a Yankin dai sun nuna su na tare da Tambuwal a 2019.
Dama dai kun ji cewa Aminu Tambuwal ya fara tadawa sauran ‘Yan takaran PDP hankali bayan da ya fito yace Gwamnonin Jam’iyyar PDP 8 su na bayan sa a zaben da za ayi watan gobe.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng