Rikicin makiyaya: Sarakunan Fulani sun bayyana ma gwamnati hanyar kawo karshen matsalar

Rikicin makiyaya: Sarakunan Fulani sun bayyana ma gwamnati hanyar kawo karshen matsalar

Lamidon rugar Fulani dake Zugobia a cikin karamar hukumar Guri ta jahar Jigawa, Isa Adamu ya roki gwamnatocin jaha data tarayya da suyi ma Allah su taimakesu su kwace makamai dake hannun yan uwansu Fulani makiyaya, inji rahoton Daily Trust.

Isa ya bayyana haka ne a yayin taron tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki da kwamitin sulhu akan rikicin makiyaya da manoma ta shirya a ranar Talata, 18 ga watan Satumba, inda yace makiyaya na kai musu hare hare a wannan yankin.

KU KARANTA: Jama’an kasar Afirka ta kudu sun cika da farin ciki yayin da gwamnati ta halasta shan tabar wiwi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Isa yana cewa makiyayan sun fito ne daga Arewacin jahar Bauchi, kuma sun shigowa yankinsu suna lalata amfanin gona tare da kai ma mutanen garin hari babu gaira babu sabar.

Sai dai Isa ya musanta batun cewa manoma sun kwace labar dabbobi suna nomawa, wanda wasu ke ganin hakan ne musabbabin rikicin dake tsakaninsu da makiyaya, inda yace babu kamshin gaskiya a wannan batu, ya kara da cewa makiyayan suna da wata muguwar manufa ne kawai.

“Rikicin makiyaya da manoma da ake fama da shi a Guri bashi da alaka da kwace labar dabbobin makiyaya, maganan gaskiya shine makiyaya dauke da bindigu, adduna, kawari da baka ne suke shigo mana garuruwanmu suna karkashe jama’a da kuma lalata gonakai.

“Muma Fulani ne, amma wadannan baki ne, don haka nake kira ga gwamnatocin jaha da na tarayya dasu taimaka mana wajen kwatar makamai daga hannuwansu, kafin lamarin ya ta’azzara.” Inji shi.

Shima a nasa jawabin, sakataren kwamitin, Rabiu Miko ya bayyana ma Fulanin cewa gwamnati ta samu korafe korafen kwace hanyoyin dabbobi da filayen kiwonsu da manoma suka yi, don haka yace ya zama wajibi gwamnatocin kananan hukumomi su tabbatar da kare hanyoyin dabbobi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel