2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP

2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP

Yan kwanaki kadan kafin zaben fitar da gwani na takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress(APC), wani jigon jam’iyyar a jihar Sokoto, Alhaji Dahiru Yusuf Yabo ya saya sheka zuwa babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Yabo ya sanar da sauya shekar nasa zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party(PDP) a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba tare da nuna goyon baya ga kudirin Gwamna Amiu Waziri Tambuwal na takarar kujeran shugaban kasa.

2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP
2019: Babban jigon APC a Sokoto ya sauya sheka zuwa PDP
Asali: Depositphotos

Yusuf Yabo wadda ya taba takarar kujeran gwamnan jhar karkashin jam’iyyar Congress for Progressive Change(CPC) a jihar Sokoto ya kaddamar da hakan yayinda yake jawabi ga dubban magoya bayansa wanda suka fito daga kananan hukumomi 23 na jihar.

KU KARANTA KUMA: Zan cigaba da yin adalci wajen nade-nade na – Buhari yayi alkawari

Tsohon kwamishinan jihar ya kasance mai daga murya akan masu sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari har zuwa lokacin da ya sauya shekar.

Yace sauya shekarsa zuwa jam’iyyar PDP yasamo asali ne bisa gazawar Shugaban kasar wajen cika alkawaran zaben da ya daukarma yan Najeriya.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Sokoto kuma dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Aminu Tambuwal, yace zai karbi sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda za’a gudanar a ranakun 5 da 6 ga watan Oktoba a Port Harcourt.

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Talata, 18 ga watan Satumba a Birnin Kebbi lokacin da ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a kokarinsa na bayyana massa kudirinsa gabannin zaben fidda gwanin, kmfanin dillancin labaran Najeriya ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel