Jama’an kasar Afirka ta kudu sun cika da farin ciki yayin da gwamnati ta halasta shan tabar wiwi

Jama’an kasar Afirka ta kudu sun cika da farin ciki yayin da gwamnati ta halasta shan tabar wiwi

Daga karshe dai gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta halasta shan tare da amfani da tabar wiwi bayan daukan tsawon lokaci ana tafka muhawara akan dacewar haka ko akasinsa.

Kamfanin jaridar TheCables ce ta ruwaito wannan labari, inda tace babbar kotun kundin tsarin mulki ta kasar ce ta halasta sha da amfani da wiwi, bayan wata kotu a kasar ta yanke hukuncin halast yin amfani da wiwi a gida a shekarar 2017.

KU KARANTA: Mutane 3,487 sun samu dubu biyar biyar na Baba Buhari a karamar hukuma daya ta Jahar Jigawa

Sai ga shi a ranar Talata, 18 ga watan Satumba babbar kotun kasar tace: “Ba zai zama laifi ba idan har mutum baligi yayi amfani da tabar wiwi a gida ba.” Inji Alkali mai sharia Raymond Zondo a yayin da take yanke hukunci.

Jama’an kasar Afirka ta kudu sun cika da farin ciki yayin da gwamnati ta halasta shan tabar wiwi
Murnar halasta shan tabar wiwi
Asali: Depositphotos

Sai dai alkalin bata fayyace iya adadin yawan wiwin da mutum zai iya amfani da shi ba a gida, amma duk da haka, hakan bai hana matasa, kungiyoyin kare hakki da kuma sauran jama’an gari fita kan titi suna bayyana farin cikinsu ba.

Guda cikin mabiya akidar shahrarren mawakin nan dan kasar Jamaica, marigayi Bob Marley da aka fi saninsa da shan tabar wiwi, Rastafarian, mai suna Prince, ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa “An dade ana cutar damu da kuma takura mana.”

A wani labarin kuma, a watan daya gabata ne shugaban kasa Canada Justin Trudeu ya tabbatar da halasta sha da ta’ammali da tabar wiwi, inda yace hakan mataki mai kyau tunda wiwi na maganin cututtuka da dama, kuma shima ya taba sha.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel