Wasu Mulhidan Najeriya sun zanta da 'yan Jarida kan tsoron lahira

Wasu Mulhidan Najeriya sun zanta da 'yan Jarida kan tsoron lahira

- Ya fara tantamar akwai Ubangiji ko babu tun a shekaru 18

- 'Idan nayi addu'a, babu biyan bukata, sai Fasto yace in ba ubangiji lokaci'

- 'Babu abinda ke nuna akwai ubangiji, kawai dai soki burutsu ne'

Wasu Mulhidan Najeriya sun zanta da 'yan Jarida kan tsoron lahira
Wasu Mulhidan Najeriya sun zanta da 'yan Jarida kan tsoron lahira
Asali: Depositphotos

Wasu mulhidai da jaridar Punch ta tattauna dasu a kudancin Najeriya:

Alfred Ayodele, Injiniya ne kuma daya daga cikin mulhidan Najeriya. Yace ya fara tantamar faruwar ubangiji tun yana makarantar babbar sakandire a shekaru 18.

Yace "Duk da ni tubabben kirista ne, akwai lokutan da nake da tambayoyi akan addinin kiristanci. Misali, Idan nayi addu'a kuma ba'a amsa ba, sai Fasto yace in kara hakuri, Ubangiji zai amsamin Idan lokaci yayi. A wannan lokacin ne na gane, abubuwan da ban roka ba nakan samesu Idan na dage."

"Sai na fara tambayar mene ne bambancin faruwar ubangiji da rashin shi, da kuma wanda ke amsa addu'a a lokacin da yake so bayan kuma a zahiri zaka iya samun komai Idan ka dage koda baka yi addu'a ba" Inji Ayodele.

Da farko kafin bullowar kafafen sadarwa na zumunta, mutane na ganin Ayodele a matsayin mai tabin kwakwalwa ne. Dangin shi ma na daukar hakan a wasa, cewa yawan ilimin kimiyya ne. Amma yanzu abin ya bambanta, tunda mutane da yawa sun gano mulhidanci ne ta kafafen yada zumunta.

DUBA WANNAN: Ko ta yaya DSS suka kasa gano Adeosun?

"Mulhidanci ba addini bane, rashin addini ne kwata kwata. Idan ina tataunawa da masu addini, nakan fahimce su tare da mutunta musu abin bauta saboda nima na taba zama irin su, toh nasan yanda zasu ji Idan na aibata musu shi," Inji Ayodele.

'Addini yana da rinjaye ga mabiyanshi balle ma a nan da ilimin kimiyya yayi karanci. Babu ubangiji, mu muke kirkirar shi da kanmu kuma muyi imani dashi' ya kara da cewa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng