Zuciyana na tare da Buhari tun a 2015 – Sanata Akpabio

Zuciyana na tare da Buhari tun a 2015 – Sanata Akpabio

- Sanata Godswill Akpabio yace mafi akasarin mambobin PDP a Akwa Ibom sun bi shi a lokacin da ya koma APC

- Yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai lashe zaben 2019 a jihar

- AAkpabio yace gwamnatin PDP bata gina kowani hanya ba a jihar lokacin da take mulki

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba yayi zargin cewa gwamnatin Peoples Democratic Party( PDP) bata taba kera kowani hanya ba a jihar Akwa Ibom cikin sekaru 16 da tayi tana mulki.

Hakan na zuwa ne yayinda ya kaddamar da cewa jam’iyyar APC mi mulki zata yi gagarumin nasara a zaben 2019 a jihar.

Zuciyana na tare da Buhari tun a 2015 – Sanata Akpabio
Zuciyana na tare da Buhari tun a 2015 – Sanata Akpabio
Asali: Depositphotos

Da yake Magana da manema labarai a jiya a fadar shugaban kasa bayan ya jagoranci wata tawagar Akwa Ibom zuwa ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa zuciyarsa ba tare da Shugaban kasar a 20015 duk da cewar shi dan PDP ne.

KU KARANTA KUMA: An bayyana ranar da majalisar Kano za ta tantance Gawuna a matsayin mataimakin gwamna

Akwabio wadda ya sauya seka zuwa jam’iyyar APC a kwanakin baya ya bayyana cewa abunda ya rage ma PDP kawai a jihar karikitai ne domin jiki da ruhin jam’iyyar sun koma APC.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai lashe jihar a zabe mai zuwa na 2019.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsofaffin yayan jam'iyya mai mulki ta APC kuma mabiya tsohon gwaman jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun sauya sheka daga APC zuwa jam'iyyar da ubangidansu ya koma ta PDP a karamar hukumar Kuje.

Da ya ke jawabi a madadin wadanda suka sauya shekar, da adadinsu ya kai 2,700, shugaban kungiyar Kwankwasiyya na yankin, Alhaji Musa Hassan Shama, ya ce sauya shekar ta su ya biyo bayan umurnin ubangidansu Sanata Kwankwaso na cewar duk magoya bayansa su koma PDP tare da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel