Shugaba mai hangen nesa ne kadai zai iya daidaita Najeriya - Saraki

Shugaba mai hangen nesa ne kadai zai iya daidaita Najeriya - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba ya bukaci ýan Najeriya da kada su nuna kabilanci wajen zabar shugabanni kawai abunda zasu duba shine hangen nesan shugaba wajen kawo chanji.

Saraki dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ya bayyana hakan a Lagas yayinda yake jawabi ga mambobin jam’iyyar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa ziyarar da ya kai sakatarioyar jam’iyyar na daga cikin rangajin da yake na neman goyon baya akan kudirinsa.

Shugaba mai hangen nesa ne kadai zai iya daidaita Najeriya - Saraki
Shugaba mai hangen nesa ne kadai zai iya daidaita Najeriya - Saraki
Asali: Twitter

Saraki ya samu rakiyan Sanata Dino Melaye, tsohon minista, Alhaji Muhammed Wakil da tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Idris Wada.

KU KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar yan Najeriya 5,000 da basu da aiki a shirin BRISIN

Darakta janar na kungiyar yakin neman zaben Saraki, Dr Doyin Okupe ma ya kasance tare da shi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

Dankwambo ya bayyana hakan a wata sanarwa da sanya hannun Dr Ayoade Adewopo, daraktan labarai na kungiyar kamfen dinsa a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel