APC ta samu baraka a Jihohin Imo, Zamfara da Yobe game da zaben 2019

APC ta samu baraka a Jihohin Imo, Zamfara da Yobe game da zaben 2019

Mun samu labari cewa ana rikici iri-iri a wasu Jihohin da ke hannun Jam’iyyar APC. Wadannan Jihohi sun hada da Zamfara, Yobe, Ogun, Imo da Yobe inda Abdul’Aziz Yari Ibrahim Gaidam, Ibikunle Amosun da kuma Rochas Okorocha su ke neman kakaba Magadan su ta karfi.

Ga dai Jihohin da rikicin kenema yayi nisa nan kamar yadda Daily Trust tayi bincike:

APC ta samu baraka a Jihohin Imo, Zamfara da Yobe game da zaben 2019
Zamfara na cikin manyan Jihohi da rikicin APC ke neman barkewa
Asali: UGC

1. Zamfara

Gwamna Abdulaziz Yari yana kokarin kakaba wani Kwamishinan sa Alhaji Mukhtar Shehu Idris a matsayin wanda zai hau kan kujerar sa. Wannan ya kawo rigima tsakanin Gwamnan da manyan ‘Yan siyasa irin su Honarabul Aminu Jaji, Alhaji Muttaka Rini, da Ibrahim Wakala. Tuni dai dama Sanata Kabiru Marafa ya raba Jiha da Gwamna Yari.

2. Yobe

A Jihar Yobe mai dai ana irin wannan rikici inda manyan ‘Yan siyasa da-dama su ka nuna rashin amincewar su da daga-hannun Mai Mala Buni da Gwamna Ibrahim Gaidam yayi. Irin su Alhaji Sidi Yakubu Karasuwa dai sun nuna cewa za su ja da yin Gwamnan a 2019. Alhaji Aji Kolom da Alhaji Ibrahim Bomoi duk su na neman nunawa Gwamnan bai isa ba.

KU KARANTA: APC ta gamu da cikas Sokoto bayan Tambuwal ya koma PDP

3. Imo

A Imo ma dai Gwamna mai-shirin barin gado Rochas Okorocha ya sha alwashi cewa sai Surukin sa Uche Nwosu ya zama Gwamna a 2019. Tuni dai Mataimakin sa Eze Madumere ya nuna masa cewa ba za ta sabu ba. Haka kuma Injiniya Chuks Ololo wanda ke auren Kanwar Gwamnan yana neman kujerar. Akwai sauran masu harin kujerar Gwamnan a APC irin su Chima Anozie.

4. Ogun

A Jihar Ogun ma dai rikici ya cabe inda Gwamna Amosun ya kakaba wani ‘Dan Majalisar Jihar Adekunle Akinlade a matsayin 'Dan takarar Gwamna a 2019. Manyan APC a Jihar fiye da 10 ba su ji dadin yadda Gwamnan ya nuna karfi wajen zaben Magajin sa ba. Irin su Otunba Bimbo Ashiru da ke Gwamnatin Amosun sun shirya bugawa da ‘Dan takarar na sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel