An gina sabon wajen horas da Sojojin sama a Najeriya

An gina sabon wajen horas da Sojojin sama a Najeriya

- Rundunar Sojin sama ta samu sabon Hedikwatar horas da Jami’an ta

- Air Marshal Sadique Abubakar ya ziyarci sabon ofishin da aka bude

- Shugaban Hafsun Sojin na kokarin karawa Sojojin saman kwarewa

An gina sabon wajen horas da Sojojin sama a Najeriya
Shugaban Hafsun Soji ya gina wasu wuraren aiki na Sojojin sama
Asali: Facebook

Mun ji cewa a cigaba da Sojin saman Najeriya watau NAF ke yi wajen ganin sha’anin tsaro na tafiya yadda ya kamata, Shugaban Hafsun Soji Air Marshall Sadique Abubakar ya kai ziyara wajen wani Hedikwatan horasa da Jami’an.

Air Marshal Sadique Abubakar wanda shi ne Shugaban Sojojin sama a Najeriya ya kai wata ziyara ta musamman har wata Makarantar Sakandare ta Sojojin sama ta Jihar Kaduna a makon da ya wuce inda ya ganewa idanun sa.

KU KARANTA: Dakarun Sojoji sun yiwa 'yan Boko Haram da suka kai masu hari kisan kiyashi

An gina sabon wajen horas da Sojojin sama a Najeriya
Shugaban Hafsun Sojin sama na kokarin gyara harkar tsaro a Najeriya
Asali: Facebook

Shugaban Hafsun Sojin ya kuma zagaya wajen Kwalejin harkar kiwon lafiya na Sojojin sama na Kasar da wata babbar Kwalejin fasaha ta Sojojin na AFIT. Babban Jami’in Sojan yayi wannan zagaye ne da sauran manyan Sojojin kasar.

Kamar yadda labari ya zo mana, babban Sojan na saman Najeriya ya ziyarci sabuwar Hedikwatar horas da Sojoji da wani filin wasa da duk su ke Kaduna inda ya tabbatar da irin kokarin da ake yi na gyara harkar tsaro musamman na sama.

Tun farkon hawan Air Marshal Abubakar kan kujerar Shugaban Hafsun Sojin Najeriya yayi alkawari cewa zai gyara gidan Sojin na sama. Kawo yanzu dai an dauki Sojojin sama fiye da 7000 bayan hawan sa wannan matsayi a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel