Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari, ya shiga takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyya mai mulki

Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari, ya shiga takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyya mai mulki

- Cif John Francis Igwe daga jihar Enugu ya shiga takarar shugaban kasa

- Dan kasuwan ya shiga tseren ne duk da cewar jam’iyyar ta tsayar da Shugaba Buhari

- Ya fito daga Ozalla karamar hukumar Nkanu west dake jihar Enugu

Duk da cewar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ta tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin dan takara guda a jam’iyyar, Cif John Francis Igwe, shahararren dan kasuwa daga jihar Enugu ya yanki fam din takara domin kalubalantar shugaban kasar wajen samun tikitin jam’iyyar.

Babban dan kasuwan ya bayyana kudirinsa a Abuja ta hannun kakakin kungiyar magoya bayansa, Mr. Mbama Mac Anthony, jaaridar The Sun ta ruwaito.

Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari, ya shiga takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyya mai mulki
Dan kasuwa ya kawo cikas a hukuncin APC kan Buhari, ya shiga takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyya mai mulki
Asali: UGC

Cif Igwe ya fito daga Ozalla karamar hukumar Nkanu west dake jihar Enugu.

Mac Anthony yace ba damuwa bane don jam’iyyar ta tsayar da Buhari. Yayi jayayya cewa yana cikin kundin tsarin mulki APC cewa suk wani mamba na da yancin neman takarar ko wani matsayi.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa wani babban limamin cocin Anglican, Steohen Oni, yace kasar nan na bukatar matashi kuma mutun mai hangen nesa da zai zamo shugaban kasar na gaba sannan kuma ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya ajiye kudirinsa na sake takara a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Kana da karfin zuciya – PDP ga Dogara yayinda ya dawo jam’iyyar

Yayi korafin cewa wasu yan siyasan Najeriya sun dade akan mulki sannan sun ki sauka daga matsayinsu domin ba matasa dama, inda ya bayyana hakan a matsayin daya daga cikin matsalolin da kasar ke fuskanta.

Bishop Oni ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da sabon shugaba da sauran jami’an cocin Cathedral Church of St Stephen, Oke-Aluko, jihar Ondo.

Yayi korafi akan ci gaba da kasancewar tsofaffin yan siyasa akan dukkanin matakai na gwamnati inda yace wasu yan siyasar ma daura kansu suke akan mulki ta karfin tuwo.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel