Allah ya yiwa jakadar Najeriya a kasar Qatar rasuwa

Allah ya yiwa jakadar Najeriya a kasar Qatar rasuwa

Jakadan Najeriya a kasar Qatar, Ambasada Abdullahi Wase ya rasu.

Sanarwar rasuwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun Ma'aikatan Harkokin Kasashen Waje, Tope Elias-Fatile a safiyar yau a babban birnin tarayya Abuja.

Wase, dan asalin jihar Filato ya rasu ne a daren jiya Juma'a a birnin Doha na Qatar bayan ya jima yana fama da rashin lafiya.

Allah ya yiwa jakadar Najeriya a kasar Qatar rasuwa
Allah ya yiwa jakadar Najeriya a kasar Qatar rasuwa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabuwar Ministan Kudi, Zainab Ahmed

Za ayi jana'izar marigayin da karfe 7 na yamma a birnin Doha da ke Qatar.

Bayan samun labarin rasuwar, Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama ya yi addu'a Allah ya jikan marigayin ya kuma bawa iyalansa da Najeriya hakurin rashinsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel