Daukar Aiki: Za mu fara tantance mabukata a ranar 24 ga watan Satumba - FRSC

Daukar Aiki: Za mu fara tantance mabukata a ranar 24 ga watan Satumba - FRSC

Hukumar kula da lafiyar manyan hanyoyi ta FRSC (Federal Road Safety Commission), ta kayyade ranakun 24 zuwa 29 ga watan Satumba na tantance mabukata da suka yi rajistar neman samun aiki watanni kadan da suka gabata.

Kakakin hukumar, Mista Bisi Kazeem, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa yayin ganawa da manema labarai a ranar Juma'ar da ta gabata.

Sanarwar da kakakin ya bayyana cikin babban birnin kasar nan na tarayya ya kuma bayyana cewa, za a gudanar da wannan tantancewa cikin dukkanin manyan birane dake jihohin kasar nan.

Daukar Aiki: Za mu fara tantance mabukata a ranar 24 ga watan Satumba - FRSC
Daukar Aiki: Za mu fara tantance mabukata a ranar 24 ga watan Satumba - FRSC
Asali: Depositphotos

Kazeem ya shawarci manema aikin hukumar akan su saurari shigowar sakonnin gayyatar su ta tantancewa cikin adireshin su shafukan yanar gizo watau email daga ranar 19 ga watan Satumba.

KARANTAN KUMA: Gwamnoni 7 dake hankoron Kujerun Sanata a Zaben 2019

Yake cewa, wannan sakonni za su kunshi bayanai dangane da tantancewar da suka hadar da; wuri, kwanan wata, lokaci da kuma ababe da ya kamata manema aikin su yi guzurin sa yayin tafiya wuraren na tantancewa.

Ya kara da cewa, ana bukatar manema aikin akan gabatar da takardun da suka ciro bayan sun kammala rajistar su ta hukumar tare da takada ta bayyana sakonni da za a turo a adirshin su na gayyatar su zuwa tantancewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel