Kashedi daga daminar bana: Madatsun ruwa na dam-dam sun tumbatsa zasu yi amai

Kashedi daga daminar bana: Madatsun ruwa na dam-dam sun tumbatsa zasu yi amai

- Daminar bana tayi albarka amma tayi barna

- An sami ambaliyar ruwa a yankuna da dama

- Yanzu kuma ana tsoron ballewar dam-dam na ruwa

Kashedi daga daminar bana: Madatsun ruwa na dam-dam sun tumbatsa zasu yi amai
Kashedi daga daminar bana: Madatsun ruwa na dam-dam sun tumbatsa zasu yi amai
Asali: Twitter

Rahotanni dake fitowa daga masu ruwa da tsaki na harkar yanayi ta Najeriya, na nuna akwai yiwuwar za'a iya samun karin ambaliyar ruwa daga ruwa daga dam dam na rafukan ruwan kogin Neja da na Binuwai wadanda suka rsatsa rabin Najeriya.

Sai dai kuma, masu yawa daga 'yan Najeriya dake zama a karkara, na yankunan da ruwan ya ratsa ne, kuma zasu ratsa matsugunansu akan wannan lamari.

A shekarar 2012, a Najeriya an sami mummunar ambaliyar ruwa, wadda ba'a taba ganin irinta ba, kuma ta janyo asarar rayuka da muhallai da dukiyoyi bilaa adadin.

Anfi zargin dumamar yanayi da jawo irin wannan matsala, domin idan iska ta dumama, tafi daukar damshi wanda ke zama hadari da gajimmare, ya kuma kawo mamakon ruwan sama.

DUBA WANNAN: Dole 'yansanda su rage tumbinsu

Shugaba Buhari ya kira ga shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA Mustapha Maihaja, ya ayyana dokar ta baci yankunan da suka fuskanci ambaliyar ruwa a kasar.

Wannan na kumshe a cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban shawara kan harkokin yada labarai malam garba shehu ya aikewa mnem labarai da safiyar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel