Tsohon gwamna ya yanke jiki ya fadi, an maza an garzaya dashi asibiti

Tsohon gwamna ya yanke jiki ya fadi, an maza an garzaya dashi asibiti

- Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya fadi warwas

- Ya fadi ne bayan taron da yayi da yan jam'iyyar ADC a Ibadan

- Nan kusa za'a sallameshi

Tsohon gwamna ya yanke jiki ya fadi, an maza an garzaya dashi asibiti
Tsohon gwamna ya yanke jiki ya fadi, an maza an garzaya dashi asibiti
Asali: Depositphotos

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Rashidi Adewolu Ladoja, ya fadi inda aka gaggauta kaishi Asibitin koyarwa dake Ibadan, babban birnin jihar.

Majiyar mu ta sanar damu cewa, Ladoja, wanda shine shugaban jam'iyyar ADC a jihar, ya fadi ne a taron sukayi domin shirin zaben kujerar gwamnan jihar Osun da za'ayi a sati mai zuwa.

An sanar da majiyar mu cewa ba wani matsanancin ciwo bane amma tabbas an kwantar dashi a asibitin Ibadan. Nan kusa za'a sallameshi.

DUBA WANNAN: Soyayya ta sa ya bata qodarsa

"Babu wani abin fargaba, domin kuwa shugaban namu zai dawo gida ranar juma'a ko asabar. Hutu kawai yake bukata." cewar majiyar mu.

An tabbatar da cewa ba' samu wani bayani akan ciwon da ke damun shi ba amma wani Dan jam'iyyar ya zargi cewa shekaru ne dake kara yawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel