Soyayya gamon jini: Miji ya baiwa matarsa kodarsa

Soyayya gamon jini: Miji ya baiwa matarsa kodarsa

- Wani mutumin kasar Saudi ya ba matar shi koda

- Tayi shekaru tana fama da ciwon

- Ba zanyi kasa a guiwa ba, indai gurin ceto rayuwar matata ne

Soyayya gamon jini: Miji ya baiwa matarsa kodarsa
Soyayya gamon jini: Miji ya baiwa matarsa kodarsa
Asali: UGC

So, kauna, tausayi da Jin kai yasa wani mutumin Saudi ya ba matar shi koda. Ya bata ne domin ya kawo karshen wahalar da take fama da ita kuma ya tseratar da rayuwar ta.

Shbeii bin Ahmad Hasan AL Shehri, ya yanke hukuncin ba wa matar shi kodai shi daya, gani da cewa ciwon yaki ci, yaki cinyewa na shekaru kuma yana son kawo karshen hakan.

Ma'auratan masu shekaru 11 da aure, anyi musu aikin ne a asibitin Sarki Fahad.

DUBA WANNAN: Pauline Tallen nason zama sanata

Mijin yace : Ba zanyi kasa a guiwa ba, gurin ganin na ceto ran matata. Bazan iya zuba ido ina ganin ta cikin ciwo ba, bayan ina da halin taimaka mata.

Al Shehri yace "yadda na ba matata wani bangare na, haka zan iya ba wanda ma ban sani ba. Ko jini na ne yayi daidai da na mabukaci, toh zan kuwa bada ba tare da wani tunani ba."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel