Wani Saraki da yayi wa mace zigidir a Kasuwa zai shekara a kurkuku

Wani Saraki da yayi wa mace zigidir a Kasuwa zai shekara a kurkuku

- Yayi niyyar yi ma wata mata tsirara a kasuwa

- Ya cire mata rigar ta da takalmi, ya barta kusan tsirara

- An yanke mishi hukuncin watanni 12 a gidan maza

Wani Saraki da yayi wa mace zigidir a Kasuwa ya zai shekara a kurkuku
Wani Saraki da yayi wa mace zigidir a Kasuwa ya zai shekara a kurkuku
Asali: Twitter

Wata kotun Majistare a Egbe, karamar hukumar Yagba ta yamma, dake jihar Kogi, ta yankewa wani mai sarautar gargajiya, Chief Stephen Fogbonjaiye, Ologun na Agidi - Ododi, wata 12 a gidan kaso sakamakon niyyar cin mutuncin wata mata a kasuwa.

An gurfanar da Fogbonjaiye, mai shekaru 70 a duniya a gaban kuliya, sakamakon tsirara da yayi wa Funmilayo Albert a kasuwa.

Abin ya faru ne a kasuwar Oja-Abu, Egbe, bayan hayaniyar da ta tara mutane tsakanin mai saida rogo da wata mata a kasuwar akan bata cika mata kudin fanke da ta siya ba.

DUBA WANNAN: Soyayyar Buhari ta jawo wa wasu

Albert ya kai wa sarkin matar da ake zargin, inda ya kwace rigar ta da takalmin ta ya kona a matsayin shi na shugaban kasuwar. Ya tabbatar da ya aikata hakan amma yace shugabancin shi ya hana fada a kasuwa. Hukuncin laifin ta kuma shine tarar carton daya na Maltina da kona kayanta.

Lauyan wanda ake karar ya roki Alkalin kotun da ya ji kan wanda ake kara saboda shekarun shi, yayayen shi da kuma dalilin ba a taba kama shi da wani laifi ba.

Mai shari'ar, Toba Olorunshola ya yanke mishi hukuncin wata 12 a gidan kaso da tarar 10,000. Zai kuma ba wacce tayi kara 8,000. Zai iya daukaka kara Idan hukuncin bai yi mishi ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel