Banbancin addini ya kai ga raba wani auren soyayya

Banbancin addini ya kai ga raba wani auren soyayya

- Auren shekaru hudu ya rabu saboda bambancin addini

- Bazan jurewa sabawa doka ba

- Aiyukan ta sun sabawa al'adata da addini na

Banbancin addini ya kai ga raba wani auren soyayya
Banbancin addini ya kai ga raba wani auren soyayya
Asali: UGC

A ranar Alhamis ne wata kotun kwastamari dake Iselin, ta raba auren shekaru hudu tsakanin Remi Atanda da Muri Atanda saboda bambancin addini.

Mai karar Muri, yazo ma da kotun bukatar a raba auren su saboda matar shi taki zuwa gurin bautar "Ifa". Yace ba zai cigaba da jurewa sabawa doka ba.

'Ifa' dai wani addinin gargajiya ne na neman sanin abinda zai faru nan gaba.

"Lokacin da mukayi aure, tare muke zuwa gurin bauta, sai watanni kadan ne da kawaye suka fara here mata kunne, shine ta bijire min."

" Nayi duk yanda zanyi in dawo da ita hanya, ta ki. Har yan uwan ta na fada ma wa amma ba canji."

DUBA WANNAN: An binne Kofi Annan

"Dole ne ta bar gidan saboda abubuwan da take sun sabawa al'adata. Abin Allah wadai ne mu zauna tare," Inji Muri.

A shugabancin shi, mai shari'a Adelodun Raheem, wanda ya fusata da rashin halartar wacce ake kara kotun, yace, hakan ya nuna dangantakar da ke tsakanin ma'auratan ta lalacewa. A don haka ne ya raba auren.

Mai shari'ar ya bada kular yara biyun da suke da ita ga Muri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel