Yawan Hayayyafa: Farfesa Osinbajo ya koka da rashin tsarin 'yan Najeriya

Yawan Hayayyafa: Farfesa Osinbajo ya koka da rashin tsarin 'yan Najeriya

- Dole Najeriya ta gina tattalin arzikin da zai zamo abin dogaro

- Yawan yan Najeriya ya kai sama da miliyan 198

- Najeriya zata zamo kasa ta uku a duniya da tafi yawan mutane

Yawan Hayayyafa: Farfesa Osinbajo ya koka da rashin tsarin 'yan Najeriya
Yawan Hayayyafa: Farfesa Osinbajo ya koka da rashin tsarin 'yan Najeriya
Asali: Depositphotos

Dole ne Najeriya ta gaggauta gina tattalin arziki da zai zamo abin dogaro ga yawan yan kasar ke hauhawa. Inji mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Ya fadi hakan ne a jawabin da yayi wa zauren shuwagabannin addini akan cigaban tattalin arzikin kasa, wanda illolin chanjin yanayin shekarun yan kasar ke kawowa.

Mataimakin shugaban kasar yace chanje chanjen suna nuna alamun cigaba da yalwatar arzikin kasar in har anyi abinda ta dace.

DUBA WANNAN: An binne Kofi Annan

Kamar yadda yace, ittifakin yan kasar ya kai sama da miliyan 198, mafi yawa a Afirka. Yace kashi 63 na yan kasar suna kasa da shekaru 25 ne, kashi 33 suna tsakanin shekaru 10 ne da 24, sai kashi 54.8 ne suke shekaru 15 da 64.

Mista Osinbajo ya kara da cewa, kashi 51 na matan kasar na shekaru 15 ne zuwa 49.

Anyi ittifakin nan da 2050 Najeriya zata zamo kasa mafi yawan mutane ta uku a duniya. Wanda Idan ba a samu tattalin arziki na dogaro ba, komai na iya faruwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel