Malam Jamilu Albani zai yi takarar Majalisar dokokin Zaria

Malam Jamilu Albani zai yi takarar Majalisar dokokin Zaria

Mun samu labari cewa wani babban Malami a Garin Zaria watau Sheikh Jamilu Abubakar wanda aka fi sani da Malam Albanin Samaru ya shirya takarar kujerar Majalisar dokokin Jihar Kaduna.

Malam Jamilu Albani zai yi takarar Majalisar dokokin Zaria
Albanin Samaru zai nemi wakiltar Samaru, Bomo, Layin-zomo a Majalisa
Asali: Original

Jama’a sun san Jamilu Abubakar a matsayin Malamin da ke karantar da addini kafin ya shiga siyasa bayan APC ta kafa Gwamnati. Tun tuni dama dai aka fara rade-radin cewa Shehin Malamin zai shiga siyasa gadan-gadan.

Sheikh Jamilu Abubakar yana neman takarar Majalisar dokokin Jihar Kaduna domin wakiltar Mazabar Basawa a 2019. Babban Malamin na addinin Musulunci zai tsaya takarar Majalisar ne a karkashin Jam’iyyar APC.

Yanzu dai har fastocin Malamin sun fara yawo kamar yadda NAIJ Hausa ta samu labari. Yanzu haka dai Malam Jamilu Abubakar yana cikin masu ba Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai shawara kan harkar addini.

KU KARANTA: Za a tantance Kwamishinan Ganduje a matsayin Mataimakin Gwamna

Jama’a sun san Jamilu Abubakar a matsayin Malamin da ke karantar da addini kafin ya shiga siyasa bayan APC ta kafa Gwamnati a 2015. Tun tuni dama dai aka fara rade-radin cewa Shehin Malamin zai shiga siyasa gadan-gadan.

Yanzu dai Mai ba Gwamnan na Kaduna shawara zai fafata da Honarabul Mukhtar Isa Hazo wanda yake kan kujerar ta Yankin Basawa. A tarihi dai ba a taba samun wanda ya zarce a kan wannan kujerar ba tun daga 1999.

Kwanaki kun ji cewa Malamin Musuluncin nan Ahmad Gumi ya fadakar da shugabannin kasar nan cewa dole akwai bukatar su rika karbar shawara daga Jama’a idan su ka hau mulki domin su ja ragamar al'umma da kyau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel