Gwamnatin Nasir El-Rufai ta samawa Matasa 257000 aiki a Kaduna

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta samawa Matasa 257000 aiki a Kaduna

Mun fahimci cewa Gwamnatin Malam Nasir El-Rufai ta samawa Matasa fiye da 25000 aiki cikin shekaru 3 da tayi a kan karagar mulki. Yanzu dai Gwamnan na neman zarcewa a kan kujerar sa a 2019.

Gwamnatin Nasir El-Rufai ta samawa Matasa 257000 aiki a Kaduna
Gwamna El-Rufai ya dauki Matasa 257000 aiki daga 2015 zuwa yau
Asali: Original

Gwamna Nasir El-Rufai wanda yake neman Jama’a su sake zaben sa a 2019 a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki ya dauki Ma’aikata 2500 aikin KASTELEA masu kula da kan hanyoyi. Mafi yawan wadanda aka dauka aikin Matasa ne.

Bayan nan kuma Gwamnatin Kaduna ta dauki Matasa akalla 13000 aikin koyarwa a Makarantu. Har wa yau wannan Gwamnatin ta APC ta samawa Matasa 3000 aikin yi a KAD-ICT ban da wasu mutum 1000 da aka dauka aiki a KADAT.

Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Gwamnatin sa ta Matasa ce masu ruwa-a-jika inda a dauki Malaman kimiyya 1200 a farkon Gwamnatin sa. Haka kuma Gwamnan ya dauki Matasa fie da 1000 aikin Likita da jinya a Jihar Kaduna.

KU KARANTA: Mai neman takara da El-Rufai ya janye shirin 2019

Kawo yanzu dai akwai Kwamishinoni 3 a Kaduna wanda duk Matasa ne shakaf. Akwai kuma mutum 40 cikin Masu taimakawa Gwamnan wanda Matasan ne. Gwamnatin El-Rufai ta kuma dauki Hadimai har 29 Matasa domin a dama da su.

Akwai kuma wasu Samari da ‘Yan mata har 16 da Gwamnan ya dauka domin a horas su zama shugabanni nan gaba. Cikin wadannan Matasa da aka dauka akwai wadanda yanzu su na cikin masu ba Gwamnan na Jihar Kaduna shawara.

Dazu kun ji cewa wani Matashi da ya fito Gwamnan Kaduna watau Jalal Falal ya fasa shiga takara a karkashin APC. ‘Dan takarar da ke neman yi wa Gwamna El-Rufai adawa ya janye zabe a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel