Kotu ta garkame wani lakcara saboda laifin luwadi

Kotu ta garkame wani lakcara saboda laifin luwadi

- Ana zargin wani lakcara na Kwallejin Noma da ke Ibadan da aikata luwadi da wani dalibinsa

- Har ila yau ana zargin lakcaran da laifin karbar cin hanci daga dalibansa domin basu makin jarabawa

An gurfanar da wani lakcara mai shekaru 40, Aremu Olufemi, a gaban kotun Majistare da ke Iyanganku a garin Ibadan bisa zarginsa da tursasawa dalibinsa yin luwadi da dashi.

Baya ga haka, ana kuma tuhumar Mr Olufemi da ke zaune a Olugbode Street, Odo-Ona a Ibadan da laifin rashawa ta hanyar tursasawa wasu dalibansa saya masa wayar salula domin ya basu makin jarabawa a kyauta.

Girma ya fadi: An kama lakcara da laifin luwadi
Girma ya fadi: An kama lakcara da laifin luwadi
Asali: UGC

Mai shigar da karar, Mattew Ojeah, ya shaidawa kotu cewa a ranar 6 ga watan Augusta misalin karfe 8.30 na dare lakcaran ya cafki al'urar wani dalibinsa mai suna Jamiu Lateef mai shekaru 27 da ke ajin farko.

KU KARANTA: Mayar da fam din takara: Buhari ya fadi dalilin da yasa ya ke neman tazarce

Wanda ake tuhumar lakcara ne da ke koyarwa a Kwallejin koyar ayyukan noma da ke Apata a Ibadan.

Ya kuma fadawa kotu cewa wanda ake tuhumar ya umurci dalibansa su saya masa Infinix Hotnote IV a matsayin cin hanci domin ya basu kyautan maki da zai sa su ci jarabawa.

A cewwar mai shigar da karar, Mr Olufemi ya yi amfani da wata daliba mai suna Ganiyat Adedeji da ke karatun Injiniyan aikin noma, ita kuma daga baya ta fadawa sauran daliban abinda malamin ya ke so.

Ojeah ya ce laifukan sun sabawa sashi na 98 (1) da 217 na dokar masu laifi ta jihar Oyo.

Sai dai malamin makarantar da ake tuhuma ya ce shi fa bai aikata laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Lauyan wanda ake zargi, J.A. Apo ya roki kotu ta bayar da belin Mr Olufemi. Alkalin kotu, Jejelola Ogunbona, ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N50,000 sannan ya daga cigaba da sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Ocktoba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel