Dukkan mu za mu hada karfi da karfe wajen tsige Buhari a 2019 – Bafarawa

Dukkan mu za mu hada karfi da karfe wajen tsige Buhari a 2019 – Bafarawa

Mun ji labari cewa ‘daya daga cikin masu shirin takarar kujerar Shugaban kasa a Jam’iyyar PDP Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayana cewa kan su ya hadu wajen ganin Buhari ya sha kasa a 2019 amma ba kuma dole ayi zaben fitar da gwani.

Dukkan mu za mu hada karfi da karfe wajen tsige Buhari a 2019 – Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Bafarawa yace dole ayi zaben tsaida 'Dan takara
Asali: Depositphotos

Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya kai ziyara Jihar Edo a makon nan inda yake cigaba da yakin neman zaben fitar da gwani da za ayi a Watan gobe har ya kuma bayyanawa manyan PDP cewa sun hadu wajen tika Buhari da kasa.

Tsohon Gwamnan na Jihar Sokoto yake cewa ‘Yan takarar sun yi yarjejeniyar cewa za su marawa duk wanda yayi nasarar samun tikitin Jam’iyya baya a zaben da za ayi. Bafarawa yace za su hada kai wajen ganin APC tayi waje a 2019.

KU KARANTA: Ko PDP ba ta bani tuta ba sai na yi kokarin ganin Buhari ya sha kasa - Atiku

‘Dan takarar na PDP ya kuma nuna cewa ba zai amince da shirin da ake yi na neman yin ittifakin tsaida ‘Dan takaran guda da zai rikewa Jam’iyyar tuta a zabe mai zuwa ba. Bafarawa yace kuma ba za su rabu da APC tayi shekara 4 nan gaba tana mulki ba.

Bafarawa ya bayyana cewa Jam’iyyar APC ta kashe kasar nan kuma dole PDP tayi kokarin wajen hana ta zarcewa kan mulki a zabe mai zuwa na 2019. Bafarawa ya kuma ce duk ‘Yan takarar kujerar Shugaban kasa a PDP sun cancanta da rike kasar nan.

Jiya kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya shirya fafatawa da irin su Bafarawa a zaben fitar da gwani da za ayi. A makon nan ne Saraki ya mika fam din sa na takarar Shugaban kasa inda yake sa ran karawa da Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel