Bayan China; Gwamnati zata sake ciwo uban bashi daga Japan

Bayan China; Gwamnati zata sake ciwo uban bashi daga Japan

- Ya hori Japan da ta bi sawun kasar China gurin hadaka da Najeriya

- Najeriya da Japan sun sa hannu a yarjejeniyar fahimtar juna

- Zamuyi farinciki Idan Japan suka shigo kamar yanda kasar China sukayi

Bayan China; Gwamnati zata sake ciwo uban bashi daga Japan
Bayan China; Gwamnati zata sake ciwo uban bashi daga Japan
Asali: Depositphotos

Gwamnatin tarayya, ta hannun ministan sufuri ya hori kasar Japan da tayi koyi da kasar China gurin hadaka da Najeriya.

Rotimi Amaechi, Ministan sufuri, ya fadi hakan a gurin sanya hannu akan yarjejeniyar fahimtar juna da Japan domin kawo cigaba a bangaren ababen more rayuwa.

Yace zamuyi matukar farinciki Idan Gwamnatin Japan zata shigo cikin mu kamar yanda Gwamnatin kasar China tayi.

Amaechi yasa hannun ne tare da ministan filaye, ababen more rayuwa, sufuri da shakatawa na kasar Japan, Tsukasa Akimoto, a ma'aikatar sufuri ta tarayya dake Abuja.

Akimoto ya taho tare da jakadan kasar Japan a Najeriya ne, Yutaka Kikuta, yace: "A matsayin ministan dake kula da ababen more rayuwa a Japan, nayi farincikin gane cewa akwai sa ran kasar Japan zata hada kai da kasar nan don gida ababen more rayuwa."

DUBA WANNAN: Afirka baza ta iya da sabuwar hannyar sadarwa ba - MTN

"Kamar yanda kuka sani, Japan na matukar kokarin samar da ababen more rayuwa masu matukar inganci. Akan hada mu da kasashe kamar China, Korea da kasashen turai.

Idan zaku tuna, ana ta tattaunawa akan hadin kan Japan da Najeriya gurin samar da titin jirgi da kuma habaka tsarin tsibirin Legas, kuma muna fatan samun damar hakan a nan gaba."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel