Afirka bata shirya wa karbar tsarin 5G ba a kan wayoyin salula - MTN

Afirka bata shirya wa karbar tsarin 5G ba a kan wayoyin salula - MTN

- Nahiyar Afirka bata shiryawa 5G ba

- A yanzu haka babu wayoyin salula masu 5G

- 5G zai samar da network mai saurin 4G ninki 50 ko 100

Afirka bata shirya wa karbar tsarin 5G ba a kan wayoyin salula - MTN
Afirka bata shirya wa karbar tsarin 5G ba a kan wayoyin salula - MTN
Asali: Original

Shugaban MTN, Rob Shuter, yace Afirka bata shiryawa network 5G ba.

Kamar yanda Shuter yace, Nahiyar zata shiryawa sabuwar kimiyyar nan da shekaru 5.

Yace "Wannan kimiyyar zata dade tana amfani. Bazata zama ta kowa da kowa ba saboda ba kowa ke bukatar shi ba. 3G ma kadai ya isa wayoyin ku".

"A yanzu haka babu wayoyi masu 5G kuma duk hanyoyin samun shi basu da yawa, ga kuma tsada. Abinda mukeyi yanzu shine koyo daga sabuwar kimiyyar amm ina tunanin 3G aka fi bukata a kasuwar mu."

5G network yana mataki na karshe na gwaji, zai samar da network mai saurin 4G ninki 50 ko 100. Zai kuma zamu abin amfani ga masana'antu da yawa.

DUBA WANNAN: Harin Ta'addanci a Paris

Afirka dai ta sami babban sauyi tun da aka sami layukan salula, wanda ya baiwa talaka damar zama dan zamani kamar kowa a kasashe masu ci gaba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel