Fiye da mutum 2000 aka kashe a Zamfara daga 2011 zuwa yau – Gwamna Yari

Fiye da mutum 2000 aka kashe a Zamfara daga 2011 zuwa yau – Gwamna Yari

Gwamna Abdulazeez Yari ya bayyana cewa daga 2011 kawo yanzu an kashe mutane sama da 2000 a cikin Jihar Zamfara. Gwamnan ya bada adadin wadanda aka hallaka a Jihar ne a makon nan.

Fiye da mutum 2000 aka kashe a Zamfara daga 2011 zuwa yau – Gwamna Yari
Gwamna Yari ya bada adadin kisan da aka yi a Zamfara
Asali: Depositphotos

Abdulaziz Yari ya tabbatar da cewa mutum sama da 2, 300 aka rasa cikin shekaru kusan 8 da yayi yana mulki Jihar Zamfara. Gwamnan ya bayyana wannan ne wajen wani taro da Gwamnati ta shirya da al’ummar Jihar a cikin Garin Gusau.

Ministan yada labarai Lai Mohammed da kuma Ministocin tsaro da na harkar ruwa watau Mansur Dan-Ali da Suleiman Adamu sun halarci taron. Yari yace rikicin ya jawo an samu ja-baya kwarai da gaske wajen harkar noma a Jihar Zamfara.

KU KARANTA: Buratai ya dauki matakin kawo karshen Boko Haram

Gwamnan ya kuma sanar da cewa an rasa tumaki fiye da 25, 000 daga lokacin da rikici ya barke a Zamfara kawo yanzu. Yari ya nuna takaicin sa ganin cewa kusan kaf mutanen Zamfara Musulmai ne amma ake samun irin wannan kashe-kashe.

Gwamna Yari yace a 2014, kaf Jihar Zamfara Sojoji ba su wuce 24 inda shi kuma Ministan labarai ya nuna cewa an fara samun saukin rikici a Yankin. Ministan tsaro na kasar ya nemi jama’a su daina fadawa masu tada rikicin asirin Jami’an tsaro.

Kwanaki kun ji cewa wani Tsohon ‘Dan Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya yace akwai rikici shigen irin na ‘Yan ta’addan Boko Haram a Zamfara wanda yayi kira da Gwamnati ta dauki mataki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel